Buhari, APC sun dauki yan Najeriya wawaye - Obasanjo

Buhari, APC sun dauki yan Najeriya wawaye - Obasanjo

A ranar Alhamis, 10 ga watan Mayu, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) dake tafiyar da mulki sun dauki Najeriya a matsayin wawaye.

Obasanjo yayi korafin cewa arzikin yan Najeriya da dama ya lalace a shekaru uku da suka shige duk da ikirarin aasin haka da Buhari da APC sukayi, yayi kira ga mutane da suyi kokarin korarsu a 2019.

Tsohon shugaban kasar wanda ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ya kuma sanar da cewa jam’iyyarsa ta Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta karbi jam’iyyar African Democratic Congress(ADC) a matsayin jam’iyyar da zata cimma mafarkinta na chnaja halin da shugabanci ke ciki a dukkan matakai a kasar cikin shekarar 2019.

Buhari, APC sun dauki yan Najeriya wawaye - Obasanjo

Buhari, APC sun dauki yan Najeriya wawaye - Obasanjo

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin

Ya kuma gargadi mutane da kada su karbi tuban jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) na son sake dawowa rayuwar yan Najeriyar.

A halin da ake ciki, Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Tanko Yakasai, ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar su za ta gudanar da gagarimin taro akan makomar siyasar yankin.

Yakasai ya kara da cewa taron, zai kunshi ‘yan siyasar yankin Arewa ne daga bangarori daban-daban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Da duminsa: Kwankwaso ya fitar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Da duminsa: Kwankwaso ya fitar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel