Abun kunya: An kama magidanci ya saci tukunyar miya

Abun kunya: An kama magidanci ya saci tukunyar miya

A yau Alhamis ne aka gurfanar da wani dan shekaru 56 mai suna Tajudeen Lateef gaban kotun Majistare da ke Ikeja bisa zarginsa da satar tukunyar miya daga shagon wata mai siyar da abinci.

Ana tuhumar Lateef da ke zaune a Atan kusa da jihar Ogun da laifin sata sai dai ya musanta zargin da ake masa.

Dan sanda mai shigar da kara Saja Mike Unah ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Mayu a shago mai lamba 27 layin Isiaka, Oko-Oba Agege a wajen garin Legas.

Abun kunya: An kama magidanci ya saci tukunyar miya
Abun kunya: An kama magidanci ya saci tukunyar miya

Ya ce wanda ake zargin ya balle shagon wanda ta shigar da karar, Tawa Amusa inda ya sace tukunya makare da miya wanda an kashe mata kudi ya kai N10,000, ya kuma sace wata waya mallakar Jamiu Onifade wanda kudin ta ya kai N3000.

KU KARANTA: Ta shiga haukan da gan-gan don kada ta biya kudin mota

"Wasu masu gadi da ke kusa da shagon ne suka damke wanda ake zargin"

Laifin da ake tuhumar sa da aikatawa ya ci karo da sashi na 287 na Dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2011, Onah ya fadawa kotu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa laifin satar na dauke da hukuncin shekaru uku a gidan kurkuku.

Alkalin kotun, Mr. A.A. Fashola ya bayar da belin wanda ake zargi a kan kudi N10,000 da kuma mutum daya da ya tsayawa wanda ake zargin.

Fashola ya ce wanda zasu tsaya wa Lateef sai sun kasance masu sana'a kuma su bayyana shaidan biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas inda ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel