Kallabi tsakanin rawwuna: Wata daliba daga jihar Katsina ta ciri ruta a jami’ar Saudiyya

Kallabi tsakanin rawwuna: Wata daliba daga jihar Katsina ta ciri ruta a jami’ar Saudiyya

Wata daliba yar asalin jihar Katsina dake karatu a jami’ar koyon likitanci na Batterjee dake jidda a kasar Saudiyya ta zamto zakakura, gwana kuma wanda tafi dukkanin daliban kwalejin hazaka, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dalibar mai suna Ummulkulthum Abubakar Sadiq ta samu digiri a karatun likitanci mai daraja ta daya, kamar yadda shuwagabannin kwalejin suka sanar a ranar yaye dalibanta.

KU KARANTA: Jana’izar Sheikh Isiyaka Rabiu: Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar hutu

Jami’ar Batterjee ta karramar Likita Ummulkulthum da wata babbar kyauta a ranar bikin yaye dalibai da jami’ar ta shirya a ranar Asabar 5 ga watan Mayu, sakamakon hazakar da ta nuna a shekarun data kwashe tana koyon likitanci a jami’ar.

Kallabi tsakanin rawwuna: Wata daliba daga jihar Katsina ta ciri ruta a jami’ar Saudiyya
Ummulkulthum da mahaifinta

Tarihin Ummkulthum ya nuna ta halarci makarantar ABC Academy, da Nurul Bayan International Academy, inda ta kammala karatunta a kwalejin Nigeria Tulic International College a shekarar 2011.

Shi ma mahaifin Likitan, Sanata Abubakar Sadiq Yaradua, tsohon wakilin al’ummar jihar Katsina ta tsakiya a majalisar dattawa, ya bayyana cewa tun a shekarar 2005 yar tasa ta yi saukan Qur’ani mai girma, inda ta haddace shi a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel