Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn

Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) zata koma sabon ofishin ta da aka kashe biliyan N24bn wajen gina shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da sabon ofishin da za a bude nan bada dadewa ba, kamar yadda aka tsara.

Mai rikon kwaryar shugabancin hukumar, Ibrahim Magu, ya bayyana jin dadin sa bisa kammala aikin ginin sabuwar shelkwatar hukumar.

Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn
Yakubu Dogara yayin ziyarar da ya kai ofishin a yau

"Ina godiya ga shugaban kasa da ya bawa wannan aiki fifiko. Hakan ya kara jadda aniyar da yake da ita ta yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Wannan gagarumin aiki ne da zai saka Najeriya alfahari da shi.

DUBA WANNAN: An kashe rayuka 9 tare da raunata mutane uku a sabon harin jihar Taraba

"Babu wani shugaba a Afrika da ya nuna zallar kishi a bangaren yaki da cin hanci kamar shugaba Buhari. Muna godiya ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati bisa goyon baya da gudunmawar da suka bamu wajen ganin aikin sabon ofishin mu ya kammala," inji Magu.

Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn
Sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn

Kazalika Magu ya mika godiya da jinjina ga majalisun Najeriya bisa damuwar da suka nuna game da ginawa hukumar sabon matsuguni.

Magu ya kara da cewa, hakan ya tabbatar da cewar hukumomin Najeriya zasu iya hada kai da juna domin yaki da cin hanci.

KARANTA: Fitacciyar 'yar siyasa ta kwashe 'yar jarida da mari

Ana saka ran mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai duba sabuwar shelkwatar kowanne lokaci daga yanzu.

Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn
Yaubu Dogara ya kai ziyara sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn

Ciki da waje: Hotunan sabuwar shelkwatar EFCC da aka gina a kan biliyan N24bn
Ibrahim Magu da Yakubu Dogara a daya daga cikin ofishin sabuwar shelkwatar

An fara gina ofishin ne a karkashin tsohuwar shugabar hukumar EFCC, Farida Waziri.

An fara ware biliyan N18bn domin ginin a shekarar 2010. Ginin na da bene hawa 10.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel