Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Magoya bayan kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da “Shi’a” yanzu haka na can garin Legas inda suke gudanar da zanga-zangar neman sakin shugaban su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da matar sa, Zeenah.

Gwamnatin Najeriya na cigaba da tsare El-Zakzaky tun bayan kama shi a shekarar 2015 sakamakon wata hatsaniya da ta afku tsakanin magoya bayan sad a dakarun sojin Najeriya.

Tun bayan garkame shi magoya bayan sa ke gudanar da zanga-zangar neman a sako shi a sassan kasar nan, musamman jihohin arewacin Najeriya, inda keda yawan musulmi.

Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas
Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Sati biyu da suka wuce an samu barkewar rikici tsakanin magoya bayan Sheikh El-Zakzaky da jami’an hukumar ‘yan sanda a Abuja yayin da suke gudanar da zanga-zanga.

DUBA WANNAN: Uwargida ta zubawa kishiyar ta gubar kashe bera a abinci kwana shida da auro ta

Wannan shine karo na farko da magoya bayan Shi’a ke gudanar da zanga-zanga a wata jihar dake kudancin Najeriya.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da manyan lauyoyi sun yi alla-wadai da cigaba da tsare Zakzaky da gwamnatin Najeriya ke yi, duk da cewar kotu ta bayar da umarnin a sake shi.

Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana a Legas

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel