Bikin gargajiya na Oro ya firgita jama'a a Legas, mata sun buya, bankuna sun rufe

Bikin gargajiya na Oro ya firgita jama'a a Legas, mata sun buya, bankuna sun rufe

A jiya, Talata, aka gudanar da wani bikin gargajiya da ake kira Oro a yankin Ikorodu dake garin Legas.

Duk da kasancewar hukumar 'yan sanda ta bayar da tabbacin babu abinda zai faru lokacin wasannin, harkoki da motsin mutane, musamman mata, sun ragu sosai a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar akwai karancin mutane da ababen hawa a kan tituna bayan rufewar bankuna a wurare da dama da suka hada da Aga, Ojubode da tashoshin mota.

Bikin gargajiya na Oro ya firgita jama'a a Legas, mata sun buya, bankuna sun rufe
Bikin gargajiya na Oro

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi, da basaraken yankin, Kabiru Shotobi, sun tabbatarwa da jama'a cewar za a yi wasannin lafiya a gama tun ranar Litinin, a wata sanarwa ta hadin gwuiwa da suka fitar.

Sanarwar ta zargi masu son haddasa fitina da yada jita-jitar da ta kai ga jama'a sun firgita da wasan gargajiyar.

DUBA WANNAN: Koyun shari'ar musulunci ta yiwa magidanci hukuncin bulala 5 saboda sakin aure

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewar hukuma zata kare kowa tare da bawa dukkan al'adu damar yin bukukuwan sun matukar ba zasu haddasa fitina ba.

Kazalika hukumar 'yan sandan ta bayyana cewar a shirye take domin saka kafar wando daya da duk wanda ya buya da sunan al'ada domin haddasa rikici.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel