Mafusatan samari sun farwa fitaccen dan siyasa don ya goyi bayan tazarcen Buhari

Mafusatan samari sun farwa fitaccen dan siyasa don ya goyi bayan tazarcen Buhari

Labarin da muka samu daga majiyar mu ta DailyTrust ta bayyana mana cewa a jiya ne dai fitaccen dan siyasar nan kuma shugaban karamar hukumar Kuje dake a birnin tarayya Abuja Alhaji Abdullahi D. Galadima tare da mataimakin sa Mista Samuel Tanko sun sha da kyar a hannun mafusatan matasa.

Haka ma kuma kamar dai yadda muka samu mafusatan matasan sun yi kukan kura sun afkawa shugabannin karamar hukumar ne biyo bayan nuna goyon bayan su ga takarar tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Mafusatan samari sun farwa fitaccen dan siyasa don ya goyi bayan tazarcen Buhari

Mafusatan samari sun farwa fitaccen dan siyasa don ya goyi bayan tazarcen Buhari

KU KARANTA: Abun da Dogara, Saraki suka tattauna da Buhari

NAIJ.com ta samu cewa matasan dai sun farwa shugabannin karamar hukumar ne yayin da suke fita daga dakin taro jim kadan bayan kammala tattaunawar su da sauran jiga-jigan jam'iyyar masu rike da mukamai.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiya sun ayyana samun nasarar cafke wasu mutane da suka ce suna gudanar da kasuwancin saye da sayarwar muggan makamai.

Kamar dai yadda muka samu, a ranar Talatar da ta gabata ne dai rundunar ta 'yan sanda ta gabatar da wadanda take zargi da aikata laifin ga 'yan jarida a harabar hedikwatar 'yan sandan dake a garin Makurdi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abinda yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie

Dalilin da yasa Saraki da Tambuwal ke fushi da Tinubu - Onuchie
NAIJ.com
Mailfire view pixel