Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell

Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell

Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya bayyana cewa idan har gwamnatin Najeriya ta ci gaba da garkame shugaban kungiyar yan Shi'a to lallai za a iya samun rikici irin na Boko Haram.

Mista Campbell, wanda mamba ne a majalisar huldar jakandancin Amurka, ya ce idan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya mutu a hannun gwamnati to "komai zai iya faruwa a kasar".

Tsohon Jakada Campbell ya ce 'yan Shi'a a Najeriya "sun yi kama da Boko Haram ta fuskar kafa gwamnati.

"Mun ga yadda gwamnatin kasar Iran ta nuna rashin jin dadinta lokacin da aka kama Zakzaky. Ba mu sani ba ko kasar na tallafawa 'yan Shi'ar Najeriya da kudade" in ji shi.

Mun san yana tsare ne a hannun gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa "gwamnatin na cewa ba za ta sake shi ba har sai gwamnatin jihar da ya sabawa ta yanke shawara, wato kenan gwamnatin jiha ce take tuhumar El-Zakzaky ba ta tarayya ba".

Mista Cambell ya bayanna wasu abubuwa biyu da ya nemi gwamnatin Najeriya ta aiwatar domin shawo kan matsalar tun kafin ta gagari kundila.

Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell
Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell

Abu na farko shi ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar Zakzaky da matarsa sun sami kulawar likitoci sosai saboda idan ya mutu a hannun gwamnati, "to babu wanda zai iya cewa ga abun da zai biyo baya".

Masanin diflomasiyyar ya ce abu na biyu shi ne gwamantin tarayya ta ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna da ta bayar da belin Zakzaky, sai kuma a jira a ga abun da shari'a za ta yi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayanna kungiyar ta IMN a matsayin haramtaciyya kuma ta hanata gudanar da taruka.

KU KARANTA KUMA: Ibrahim Magu ya gana da Shugaban Majalisa Saraki a sabon ofishin EFCC

Idan dai bazaku manta ba kimanin sama da shekara biyu kenan gwamnatin Muhammadu Buhari na tsare da Zakzaky da matarsa a wani kebabban wuri da ba a bayyana ba, duk da cewa kotuna da dama sun bayar da belinsa.

A watan da ya wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel