Ibrahim Magu ya gana da Shugaban Majalisa Saraki a sabon ofishin EFCC

Ibrahim Magu ya gana da Shugaban Majalisa Saraki a sabon ofishin EFCC

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki sun hadu da Shugaban Hukumar EFCC Mista Ibrahim Magu lokacin da ya zagaya sabon Hedikwatar Hukumar mai yaki da masu yi wa tatallin arzikin kasa zagon kasa.

A jiya Talata ne Jami’an Hukumar EFCC su ka zagaya da Shugaban Majalisar kasar domin ganewa idanun sa katafaren sabon ofishin da aka gina. Bukola Saraki ya yabawa kokarin da aka yi wajen ginin ya kuma yi alkawarin bada goyon baya.

Bukola Saraki yake cewa ya ji dadin ganin yadda aka gina Hedikwatar kuma abin burgewa ma shi ne daga Najeriya aka samu wanda ya zana ginin. Shugaban Majalisar yace duk da banbancin ra’ayin da ke tsakanin su za su marawa Hukumar EFCC baya.

Ibrahim Magu ya gana da Shugaban Majalisa Saraki a sabon ofishin EFCC
Shugaban EFCC Magu ya gayyaci Saraki domin ganin ginin EFCC

KU KARANTA: Kungiyar Izala ta ziyarci wani babban Gwamna

Saraki yake cewa babban abin da ake bukatar ayi magani a kasar nan shi ne satar dukiyar jama’a da rashin gaskiya. Saraki yace duk surutun da ake yi Majalisa tayi bakin kokarin ta wajen ganin an zuba kudin da ya kamata na kammala wannan gini.

Tun kwanaki kun ji cewa an fara wannan aiki a Birnin Tarayya Abuja. Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki yace a makon gobe za a bude wannan Hedikwata domin fara aiki. A kwanaki dai an ta takaddama tsakanin Saraki da EFCC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel