Uwargidan Shugaban Kasar Brazil ta tsundama cikin wani Tafki domin ceto Karen ta

Uwargidan Shugaban Kasar Brazil ta tsundama cikin wani Tafki domin ceto Karen ta

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa uwargidan shugaban kasar Brazil, Marcela Temer, ta yi kukan kura ta tsunduma cikin wani tafki dake fadar shugaban kasar domin ceto karen ta da ta saba kiwon sa.

Legit.ng ta fahimci cewa wannan lamari ya sanya batutuwa da musayar ra'ayoyi akan ta su suke ta kwaranya a kafofin watsa labarai da dandalan sada zumunta.

Fitacciyar uwargidan mai shekaru 34 a duniya da ta shahara da kyawun sura da kuma sifa ta tsunduma cikin tafkin ne bayan da karen ta mai sunan Picoly ya afka cikin sa yayin bibiyar wasu agwagi kuma ya gaza fitowa.

Uwargidan Shugaban Kasar Brazil; Marcela Temer
Uwargidan Shugaban Kasar Brazil; Marcela Temer

Wannan lamari mai ban mamaki gami da kamanceceniya ta wasan kwaikwayo ya afku ne a ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, wanda sai a wannan mako rahoton ya bazama a duniya.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kai hari a Gidan wani Mai Gari a jihar Filato

Kafofin watsa labarai na kasar ta Brazil sun yi ba'a dangane da wannan jarumta ta uwargidan shugaban kasar da ya sanya rahoton ya kasance kanin labarai da abin fade cikin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.

A yayin haka kuma rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar na Brazil, Michel Termer shine shugaban kasa mafi kasa ta fuskar shahara a tarihin shugabannin da suka shude.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel