Takaitaccen Tarihin marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu da ya rasu a ranar Talata

Takaitaccen Tarihin marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu da ya rasu a ranar Talata

A ranar Talata, 8 ga watan Mayu ne Allah yayi ma shahararren Malamin nan kuma, fitaccen Attajiri, Sheikh Isiyaka Rabiu rasuwa, wanda ya rasu a birnin Landan a wani babban Asibitin da yayi fama da wata gajeruwar jinya.

Legit.ng ta tattaro muku wasu muhimman bayanai game da tarihin fitaccen Shehin Malamin, kamar haka;

KU KARANTA: An sake kwatawa: Sojoji sun cika hannayensu da wasu yan bindiga guda 6 a jihar Benuwe

1- A shekarar 1928 aka haifi Isiyaka Rabiu, sunan mahaifinsa, Muhamamdu Rabiun Dan Tinki

2- Mahaifin Isiyaka Rabiu dan asalin garin Bichi ne kuma fitaccen Malamin addini ne

3- Isyaka Rabiu yayi karatun Qur’ani da Ilimin Larabci a hannun mahaifinsa, daga shekarar 1936 zuwa 1942

Takaitaccen Tarihin marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu da ya rasu a ranar Talata
Sheikh Isiyaka Rabiu tare da Ganduje

4- Isiyaka Rabiu ya cigaba da yawon neman ilimi zuwa garin Maiduguri na jihar Borno

5- A shekarar 1949 Malam Isiyaka Rabiu ya fara karantarwa a matsayinsa na cikakken Malamin Qur’ani da Larabci

6- A shekarar 1952 Malam Isiyaka Rabiu ya kafa kamfanin ‘Isiyaku Rabiu & Sons, suna harkar atamfofi

7- Isiyaka Rabiu dan jam’iyyar NPN ce tasu tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari

8- Malam Isiyaka Rabiu ne halastaccen Khalifan Sheikh Ibrahim Nyass, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

9- Daga cikin Yayansa akwai hamshakan Attajirai da suka hada da Abdul Samad da Rabiu Isiyaka Rabiu

Da fatan Allah ya jikansa da gafara, ya bashi ladar hidimar da yayi ma addinin Muslunci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel