Hanyoyi biyu da motsa jiki kan iya hallaka mutum

Hanyoyi biyu da motsa jiki kan iya hallaka mutum

Tsawon shekaru da dama masana lafiya na bawa mutane shawarar suke motsa jiki domin samun koshin lafiya.

Saidai motsa jiki fiye da kima kan iya cutar da mutum ko ma ya hallaka shi.

Ga wasu hanyoyi biyu da motsa jiki kan iya hallaka mutum.

1. Rhabdomyolysis

Wani yanayi ne mai muni da jiki yake fadawa sakamakon motsa jiki. Wannan yanayi ya fi samun masu dauka abubuwa masu nauyi ko masu shigar tsere da suke gudu fiye da kima da yake kai ga ruwan dake jikin mutum ya kone.

Rhabdomyolysis da ake kira da rhabdo na faruwa ne yayin da ruwan jiki ya kone har ta kai wasu sinadarai nau'in protein (myoglobin) sun shiga cikin jini. Sinadaran na lalata kodar mutum har ta kai ga sun daina aiki.

Hanyoyi biyu da motsa jiki kan iya hallaka mutum
Hanyoyi biyu da motsa jiki kan iya hallaka mutum

Kowanne nau'in motsa jiki dake sa kwanji yawan motsawa kan iya haddasa matsalar rhabdo.

2. Gushewar ruwa a jiki (Dehydration): Rayuwar jikin mutum ta dogara ne kacokan a kan wasu sinadarai masu ruwa-ruwa.

DUBA WANNAN: Kungiyar izala ta ziyarci gwamna Bello, ta jinjinawa wani namijin kokari da ya yi

Jiki kan rasa ruwa da ragowar sinadarai dake da ruwa-ruwa sakamakon motsa jiki.

Jikin mutum na bukatar ruwa a kalla lita 2.5 kullum saboda ruwan dake fita daga jiki sakamakon fitsari da gumi.

A yayin gasar tsere da wasannin Common wealth da aka gudanar a Australia, 'yar wasan tseren kasar Scotland, Callum Hawkins, ta fadi wan-war yayin da ya rage mata kilomita kadan ta kai ga nasara saboda karewar ruwan jikin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel