Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina - Sani Moda

Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina - Sani Moda

- A yayin zantawar da manema labarai suka yi da shahararren jarumin finafinan Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani cewar ya rasu a daren jiya Litinin

Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina - Sani Moda
Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina - Sani Moda

A yayin zantawar da manema labarai suka yi da shahararren jarumin finafinan Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani cewar ya rasu a daren jiya Litinin.

DUBA WANNAN: Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas

Sani Moda ya kara da cewa ya yi mamakin yadda labarin mutuwar tasa ta yadu, wanda a dalilin hakan yake ta faman shan kira daga ciki da wajen kasar nan daga wurin masoyan sa, domin tabbatar da gaskiyar al'amarin. A cewar shi, an sami kuskuren sanarwar ne daga asibitin da yake kwance, inda suka bayyana shine a matsayin wanda ya rasu, ya bayyana cewar bashi Allah ya amshi rayuwar tasa ba na kusa dashi ne ya amsa kiran Allah. Sannan kuma ya bayyana cewar yana cigaba da samun lafiya.

A jiya ne dai kafafen yada labarai suka dinga yada cewar Allah yayi wa fitaccen jarumin rasuwa, bayan ya jima yana fama da jinya. Muna masa adu'ar Allah ya bashi lafiya mai inganchi yasa kuma hakan ya zama kaffara ce a gare shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel