Turawa sun bukaci a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani

Turawa sun bukaci a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani

- Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba da tofin Allah tsine kan da'awar da tsohon shugaban Faransa,Nicolas Sarkozy da wasu gungun mutane 300 suke yi na a gaggauta share duk wasu ayoyin da ke sukar Yahudawa da Kiristoci daga Al Kur'ani mai tsarki.

Turawa sun bukaci a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani
Turawa sun bukaci a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani

Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba da tofin Allah tsine kan da'awar da tsohon shugaban Faransa,Nicolas Sarkozy da wasu gungun mutane 300 suke yi na a gaggauta share duk wasu ayoyin da ke sukar Yahudawa da Kiristoci daga Al Kur'ani mai tsarki.

A jerin mutanen da ke sahun gaban wajen yin wannan farfagandar akwai,tsohon shugaban kasar Faransa,Nicolas Sarkozy,Philippe Val, tsohon shugaban jaridar "Charlie Hebdo" wacce daman ta yi kaurin suna wajen yin zanen batanci kan mafificin halitta,Manzon Allah Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,tsohon magajin garin birnin Paris,Bertrand Delanoe,tsaffin ministoci 3,jiga-jigan addinai daban-daban, masana,taurarun fina-finai,masu aikin hannu da dai sauran su.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

Masu bakar da'awar suka ce,

"A gaggauta share duk wasu ayoyin da ke kiran Musulmai da su kyamaci ko kuma su yaki Yahudawa da Kiristoci.Saboda barin su, babbar barazana ce ga rayuwar mabiya wadannan addinan".

Kamar a sauran sassan duniya, samun wannan labarin ke da wuya,shugabannin kasar Turkiyya suka yi tofin Allah tsine da kuma tsawatawa Farasansawan.

A shafinsa na Twitter,mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim Kalin ya ce,

"Al Kur'ani,littafi ne mai tsarki.Allah zai ci gaba da tsare shi har karshen duniya.Al Kur'ani ba allo ba ne da za a dinka rubutu kansa,kana a dinka goge shi a duk lokacin da aka ga dama.Littafinmu ne mai tsarki.Kyamar Yahudawa akida ce da ta bulla a tsakiyar Turai.Turawan da ke bukatar warware bakin zaren wannan matsalar, sun waiwayi baya don bincikar tarihinsu.Babu wani jahilci da ya kai wannan bukatar tasu,a wannan duniyar tamu ta yau,inda ake tinkaho da wayewa".

Mataimakin shugaban gwamnatin Turkiyya,Bekir Bozdağ ma ya wallafa albarkacin bakinsa a Twitter inda ya ce,

"Daya daga cikin manya-manyan makiyan Islama,tsohon shugaban Faransa da wasu gungun Faransawa 300 sun shafa wa Islama bakin fenti ta hanyar bayyana bukatarsu ta a gaggauta cire "Ayoyin da ke kiran jama'a da su kyamaci Yahudawa da Kiristoci" daga Kur'ani.Wadannan su ne shashashu,sakarkaru,marasa tunani,gidadawa,dangin Abu Jahil, kana 'yan DAESH a Yamma.Ba Sarkozy ba,ko da illahirin makiya Islama za su hade mana kai,ba zasu taba kawo daidai da aya daya tilo ko kuma sauya wani abu daga cikin Kur'ani, har sai an busa kaho".

Ministan harkokin wajen Turkiyya,Mevlüt Çavuşoğlu kuma cewa ya yi,

"Wannan wata alama ce da ke nuna irin yadda kyama da nuna wariya ga Musulmai suka kamari a Turai.Tuni wadannan mutane suka wuce gona da iri. Shin me kuke tsammanin zai afku, bayan da suka furta irin wadannan kalaman ? Za a dinka kai wa masallatai hare-hare a Turai.A tsawon tarihinku kun ci gaba da zaluntar Yahudawa.Musulmai ne suka cece su ta hanyar karbar bakwancinsu hannaye biyu a tsawon karnoni da dama, musamman ma a zamanin daular Musulunci ta Usmaniyya,inda aka kare martabarsu tare da karrama su.Bamu san me ake nufi da kyamar Yahudu ba.Don babu irin wannan akidar a addini da kuma littafinmu.Yayin da a yau, a Turai nuna wariyar launin fata,kyamar masu neman mafaka da 'yan gudun hijira da kuma waninsa, ke ci gaba da samun gindin zama.Jam'iyyun siyasa masu wariyar launin fata na cin karansu babu babbaka a kasashenku.In dai da gaske kuke,ku fara yakar su mana.Shin wanne ne 'yancin da kuke ambato? Shin wa zaku bai wa darasi? ".

Ministan yawon bude ido da raya al'adu na Turkiyya,Numan Kurtulmuş ma, ya nuna bacin ransa inda ya ce,

"Wannan batun da suka zo da shi ba komai ba ne face, gidadanci da kuma wauta.Allah wadai ga wadanda ke sukar mabiya wannan tsarkaken littafin "Kur'ani" da kuma wannan babban addinin mai suna salama "Islam".Ina fatan al'umar kasashen Turai zasu yi kunnen uwar shegu da wadannan maganganun na badala da rashin hankali".

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel