Yadda Atiku Abubakar ya hana ni zama gwamnan Adamawa a 1991 - Boss Mustapha

Yadda Atiku Abubakar ya hana ni zama gwamnan Adamawa a 1991 - Boss Mustapha

Kimanin shekaru 28 da suka shude, Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Mista Boss Mustapha ya yi bayanin yadda yace tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya shirya masa kullalliyar da ta hana shi zama Gwamnan Adamawa.

Kamar dai yadda Boss Mustapha din ya ayyana, biyo bayan sabanin da suka samu da fitaccen dan siyasar Atiku lokacin da ya nemi ya kakaba masa mataimaki, sai kawai ya juya masa baya ya hada kai da jam'iyyar adawa.

Yadda Atiku Abubakar ya hana ni zama gwamnan Adamawa a 1991 - Boss Mustapha
Yadda Atiku Abubakar ya hana ni zama gwamnan Adamawa a 1991 - Boss Mustapha

Legit.ng ta samu cewa Mista Boss Mustapha yayi wannan bayanan ne lokacin da yake jawabi yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar ta Adamawa.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yake tunanin shine ya sanya 'yan kabilar yarbawa basu zabe sa ba a zaben 1999.

A cewar Cif Obasanjo, yana tunanin saboda ya ki ya shiga kungiyar nan ta hadaddiyar kabilar yarbawan dake kare muradun su ta Afenifere da Marigayi Sanata Abraham Adesanya yake shugabanta a wancan lokacin ne ya janyo hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel