Guguwar Iska ta kashe Mutane 76 a Kasar Indiya

Guguwar Iska ta kashe Mutane 76 a Kasar Indiya

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kimanin rayuka 76 ne suka salwanta tare da jikkatar da dama a yayin da wata guguwar iska mai tsananin karfi dauke da kura ta afku a jihohin Rajasthan da Uttar Pradesh dake Arewacin kasar Indiya.

A rahoton babbar kafar watsa labarai ta BBC, wannan guguwa mai matsanancin karfi da ta afku a ranar Larabar da ta gabata ta tarwatsa gidaje, lalata wutar lantarki, cizge bishiyu daga saiwoyin su gami da salwantar rayukan dabbobi na kiwo.

Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin rayukan mutanen da suka salwanta sun gamu da ajali ne yayin da suke kwan-kwance inda gidajen su suka rufta a kansu.

Guguwar Iska ta kashe Mutane 76 a Kasar Indiya
Guguwar Iska ta kashe Mutane 76 a Kasar Indiya

Hukumomin kasar ta Indiya sun bayyana cewa, afkuwar guguwar iska mai karfin gaske ba sabon abu bane a kasar, sai dai wannan barna da ta janyo a wani lokaci ya yiwa na sauran lokutan baya fintinkau.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Wata Kungiyar Matasa ta tallafawa Marayu kayan Makaranta a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, barnar da wannan tsautsayi ya janyo ta fi ta'azzara a gundumomi uku dake garin Rajasthan inda kimanin rayuka 31 suka garzaya makoma ta gaskiya.

Wannan lamari dai ya sanya an rufe makarantun yankin da ibtila'in ya afkawa, yayin da Ministan yankin Rajasthan, Vasundhara Raje ya bayyana cewa tuni ma'aikata sun dirfafi yankunan da abin ya shafa domin fara gudanar da agaji na gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel