Hukumar Alhazai Reshen Jihar Kano ta bayyana adadin Kudin Kujerun bana

Hukumar Alhazai Reshen Jihar Kano ta bayyana adadin Kudin Kujerun bana

Hukumar jin dadin Alhazai ta kirayi maniyyatan jihar Kano akan su gaggauta cika kudaden kujerun su kafin lokaci ya kurace yayin da ta kayyade adadin kudin kujerun na bana wanda aka samu rangwami na wani kaso a wannan shekara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar ta kayyade adadin kudi na N1, 474, 167.25 a matsayin kudin kujerun maniyyatan jihar Kano na bana.

Babban Sakataren hukumar reshen jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai inda ya ce an samu rangwami na N63, 972.72 a kudin kujerar bana.

Hukumar Alhazai Reshen Jihar Kano ta bayyana adadin Kudin Kujerun bana
Hukumar Alhazai Reshen Jihar Kano ta bayyana adadin Kudin Kujerun bana

Dambatta ya bayyana cewa, wannan shine karo na farko cikin kimanin shekaru 10 da aka samu rangwami na kudin kujerar sabanin yadda a duk shekara kudin yake tumfayawa.

Ya kuma kirayi maniyyatan da suka riga da da kammala biyan kudaden kujerun su akan su garzayo hukumar domin karbar rara na rangwami da aka samu a bana.

KARANTA KUMA: Hotunan yadda aka gudanar da murnar Ranar Ma'aikata a garin Ibadan

Ya kara da cewa, hukumar tuni ta kammala shirye-shirye na tanadin masaukai ga maniyyatan a wurare dake kusa da masallatai na harami a biranen Makkah da Madinah.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar jin dadin Alhazai ta kasa ta bayar da kasafin kujeru 5,500 ga maniyyatan jihar Kano a bana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel