Shugaba Buhari ya aikawa matasan Najeriya da muhimmin sako, ya masu alkawari

Shugaba Buhari ya aikawa matasan Najeriya da muhimmin sako, ya masu alkawari

- Shugaba Buhari yayi kira ga matasan Najeriya dasu shiga cikin harkar noma

- Shugaban kasar yace akwai ayyuka da dama bangaren na harkar noma

- Shugaban yace kamfaninnikan aikin gona shida sunce zasu bunkasa harkokinsu zuwa Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya aikowa matasan Najeriya da sako, inda ya bukacesu dasu koma harkar noma saboda nan ne inda kasar ta dosa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kamfaninnika shida na ayyukan gona a kasar Amruka, a ranar Litinin 30 ga watan Afirilu.

Shugaba Buhari ya aikawa matasan Najeriya da muhimmin sako, ya masu alkawari

Shugaba Buhari ya aikawa matasan Najeriya da muhimmin sako, ya masu alkawari

Bayanin ya fito ne daga bakin Garba Shehu wanda shine babban mai bawa shugaban kasar shawara ta fannin sadarwa, a ranar Talata 1 ga watan Mayu, inxa ya bayyana cewa shugaban kasar yace akwai ayyuka da dama a harkar noman.

KU KARANTA KUMA: Bayan ganawa da Trump, shugaba Buhari ya bar Washington DC

Yace ganawarsa da kaninnikan shida na kasar Amruka zai kawo cigaba sosai a Najeriya, saboda suna shawarar bude rassa a nan gida Najeriya, wanda hakan zai samarwa matasan da dama ayyukanyi.

A halin da ake ciki, Jam'iyyar PDP ta soki ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Amurka.

Ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya kunyata Najeriya a ziyarar, cewa ya kasa tallata kasarsa a gaban manyan jami'an gwamnatin Amurka.

Sakataren Jam'iyyar na kasa, Kolawale ya ce a lokacin tattaunawa da Shugaban Amurka, Donald Trump shugaba Buhari ya ki fitowa fili ya yiwa Amurka tayin ci gaba da sayen danyen man fetur da Najeriya ke samarwa bayan ta dakatar da sayen man.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansanda ya canza ma rundunar Yansandan SARS suna, karanta

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel