Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: An samu tashin bama bamai a garin Mubi

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: An samu tashin bama bamai a garin Mubi

Legit.ng ta samu rahoton tashin bama bamai a unguwar Yan Gwanjo dake cikin garin Mubi, kamar yadda wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Sani Abdullahi ya tabbatar.

Majiyar na mu ya tabbatar da cewar karar tashin bama bamai biyu suka ji, inda ya kara da cewa guda daya ya tashi ne a cikin wani Masallaci, yayin da dayan kuma ya tashi a wajen Masallacin.

KU KARANTA: Yansanda sun sako Shehu Sani bayan ya amsa gayyatarsu game da zargin tafka laifin kisa

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: An samu tashin bama bamai a garin Mubi
Rahoton

Wannan hari yazo ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amsa gayyatar shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa kasar Amurka, inda suka tattaunawa batutuwan da suka shafi matsalolin ta’addanci a Najeriya.

A wani labarin kuma Najeriya ta biya dala miliyan 400 ga gwamnatin kasar Amurka don siyan jiragen yaki na zamani guda 12 a wani mataki na kara kaimi da yakin da rundunar Sojojin Najeriya ke yi da yan ta’adda Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel