Ku yafe min idan nayi maku wani laifi - Gwamna Bindow ya nemi gafarar jam'iyyar APC

Ku yafe min idan nayi maku wani laifi - Gwamna Bindow ya nemi gafarar jam'iyyar APC

- Gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla ya nemi afuwar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Adama

- Bindow ya nemi afuwar ne a jiya yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar domin tattauna zaben shugabannin jam'iyyar

- Gwamna Bindow ya ce ba shi da wani dan takara tare da bukatar masu son yin takara da su fita domin neman goyon bayan 'ya'yan jam'iyyar

Gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow, ya nemi afuwar jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a cikin jam'iyyar.

"Idan na yiwa wani daga cikin ku laifi don Allah ya yafe min. Ba zan taba batawa wani daga cikin ku da gan-gan ba," gwamna Bindo ya fadawa iyayen jam'iyyar APC a jihar Adamawa.

Bindow ya nemi dukkan 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Adamawa da su yafe shi idan ya bata masu rai.

Ku yafe min idan nayi maku wani laifi - Gwamna Bindow ya nemi gafarar jam'iyyar APC
Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow

Gwamnan na wadannan kalamai ne a jiya, Litinin, yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Yola, babban birnin jihar.

Bindow ya tabbatar wa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar cewar bashi da wani dan takara a cikin masu neman shugabancin jam'iyyar tare bayyana cewar ya fada wa masu burin yin takara su fita su nemi goyon bayan 'ya'yan jam'iyya.

"Gwamnati na a shirye take tayi aiki da duk wanda Allah ya bawa nasara," Bindow ya fada.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe

Da yake tofa albarkacin bakin sa yayin taron, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya jaddada bukatar bin dokokin jam'iyya yayin gudanar da zaben.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, ya soki masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a kan yin burus da batun raba mukamai zuwa sassan jihar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel