Dakatad da Omo-Agege ya sabawa doka – Ministan Shari’a, Malami

Dakatad da Omo-Agege ya sabawa doka – Ministan Shari’a, Malami

Babban kauyan Najeriya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, a yau Litinin ya bayyanawa babban kotun tarayya da ke Abuja cewa dakatad da Sanata Ovie Omo-Agege, da majalisa tayi ya sabawa doka.

Wannan na daga cikin jawabin da ofishin ministan ilimi ta gabatar a kotu bisa ga karar da Omo-Agege na kalubalantar dakatad da shi.

Amma wakilin shugaba majalisan dattawa, Mr. Mahmud Magaji (SAN),ya musanta wannan abu.

Mr. Mahmud Magaji (SAN) ya ce Sanatan shi kanshi mamban kwamitin masu dakatad da sanatoci ne kuma wajibi ne a hukunta shi.

Dakatad da Omo-Agege ya sabawa doka – Ministan Shari’a, Malami

Dakatad da Omo-Agege ya sabawa doka – Ministan Shari’a, Malami

Yayinda wakilin gwamnatin tarayya kuma sakataren din-din-din na ma’aikatar Shari’a, Mr. Dayo Apata, ya yi kira ga kotu tayi watsi da dakatad da Omo-Agege da majalisa tayi.

Justice Nnamdi Dimgba ya dakatad da wannan kara zuwa ranan 10 ga watan Mayu domin sanin gaskiyan al’amari.

KU KARANTA: Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa majalisan dattawa ta dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege sanadiyar sukan abinda majalisar tayi na kokarin sauya fasalin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar
NAIJ.com
Mailfire view pixel