Kalli bidiyon yadda Jirgin Sojojin Najeriya yayi lugudan wuta kan ƴan Boko Haram

Kalli bidiyon yadda Jirgin Sojojin Najeriya yayi lugudan wuta kan ƴan Boko Haram

- Sojojin Najeriya son samu gagarumar nasara kan yan Boko Haram

- Sojojin dai sun yi amfani ne da jirgin yakinsu waje kaiwa yan ta'addan hari a wani babban sansaninsu

Rundunar Sojin Najeriya karkashin atisayen Lafiya Dole, sun yiwa ƴan Boko Haram ruwan wuta a ƙauye Yuwe na jihar Borno.

A wani bidiyo da Sojin saman suka fitar a shafinsu na Facebook, ya nuna yadda jirgin yayi shawagi kamar tsunstu a sama, bayan ya gama kyallara ido ya hango su, nan take jirgin yayi lugudan wuta a kan gidajensu da motocinsu da duk abubuwan da suka tanada a sansanin nasu.

Rundunar dai ta ce, bidiyon anyi shi ne a ranar 28 ga watan Afrilu, kuma ya samu gagarmar nasara.

KU KARANTA: An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda ƴan ta'addan suke ta yunƙurin guduwa domin tsira da rayuwarsu, amma Sojojin cikin salo na nuna bajinta da kwarewar sarrafa jirgin yaki sanfurin Mi 35 , suka riƙa yi musu ruwan wuta.

Jirgin Sojojin Najeriya yayi lugudan wuta kan ƴan Boko Haram

Jirgin Sojojin Najeriya yayi lugudan wuta kan ƴan Boko Haram

Waɗansu tsirari da ake iya gani sun gudu domin neman mafaka bayan sun samu raunuka a jikin, jirgin Sojojin bai kyale su ba, sai da ya ƙara binsu ya zazzaga musu harsashi. Kamar yadda sanarwar da kakakin rundunar sojin saman Olatokunbo Adesanya ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel