Zan binciki Buhari idan na zama shugaban kasa - Atiku

Zan binciki Buhari idan na zama shugaban kasa - Atiku

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce zai binciki gwamnatin Buhari idan yayi nasarar zama shugaban kasa bayan zaben 2019

- Atiku ya ce abin dubawa ne yadda gwamnatin ta tade tana yaki da Boko Haram amma har yanzu ba'a magance su ba

- Atiku kuma ya zargi shugaba Buhari da kare wadansu mutane daga fuskantar shari'ah

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, kuma mai neman tsayawa takaran shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2019 ya ce zai gudanar da bincike a kan cinikin makamai da gwamnatin shugaba Buhari take saya.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa a yau Asabar, turakin Adamawan yace an dauki lokaci mai tsawo ana ta artabu da yan kungiyar ta Boko Haram amma har yanzu ba'a kawo karshen matsalar ba.

Atiku zai binciki shugaba Buhari
Atiku zai binciki shugaba Buhari

KU KARANTA: Nifa ban ce a tsige shugaba Buhari ba - Sanata Urhoghide

"An kwashe shekaru takwas ana yaki da yan kungiyar Boko Haram duk da cewa basu da wani cikakken horo na musamman," inji shi.

"Ina son zama shugaban kasar Najeriya, saboda akwai wasu abubuwa da nake da niyyar aiwatarwa amma ban samu dama ba lokacin da nake mataimakin shugaban kasa a Najeriya, zan kuma binciki yadda gwamnati ta gaza kawo karshen rikicin Boko Haram na tsawon shekaru, zan kuma binciki batun siyan makamai da wannan gwamnatin ta sayo."

Bugu da kari, Atiku ya ce zai magance cin hanci da rashawa inda ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da kare wasu mutane wadanda ya kamata su fuskanci shari'a.

idan yan Najeriya basu manta ba, gwamnatin mu ne ta kafa hukumar yaki da rashawa (EFCC), kuma nine na samar da kudaden da hukumae EFCC ta fara amfani dashi bayan kafa ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel