Ranar ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Ranar ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar bayar da hutu ga daukacin 'yan Najeriya musamman ma ma'aikata a ranar Talata mai zuwa da ke dai-dai da daya ga watan Mayu shekarar 2018 domin shagulgulan zagayowar ranar ma'aikata.

Babban ministan harkokin cikin gida Laftanal Janar Abdurrahman Dambazau (mai ritaya) shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sa da ya fitar a garin Abuja.

Ranar ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Ranar ma'aikata: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

KU KARANTA: Yan majalisa 5 da suka so a tsige Buhari

NAIJ.com ta samu cewa a cikin sakon, ya kuma jinjinawa daukacin ma'aikatan kasar bisa jajircewar su wajen tabbatar da ginuwar Najeriya.

A wani labarin kuma, Kungiyar kiristoci ta Najeriya baki daya ta sanar da kudurin ta na gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su ga gwamnatin tarayyar Najeriya game da cigaban aukuwar hare-haren makiyaya a wuraren ibadar su ranar Lahadi mai zuwa.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyar yanzu haka tana ta kara sanar da mabiya addinai a dukkan majami'un kasar nan da ma sauran masu fada aji da su fito kwansu-da-kwalkwata domin gudanar da zanga-zangar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel