‘Yan Majalisa sun nemi Sufetan ‘Yan Sanda yayi masu bayani game da sha'anin tsaro

‘Yan Majalisa sun nemi Sufetan ‘Yan Sanda yayi masu bayani game da sha'anin tsaro

A jiya Majalisa ta zauna inda ta tattauna game da sha’anin tsaron cikin gida da yake kara tabarbarewa. Majalisar Dattawa ta dauki matakin cewa Sufetan ‘Yan Sandan kasar zai hallara gaban ta domin yi mata gamsashhen jawabi.

‘Yan Majalisa sun nemi Sufetan ‘Yan Sanda yayi masu bayani game da sha'anin tsaro
Wasu Sanatoci sun koka da matsalar da ke Benuwe da sauran Jihohi

Ko da dai wasu Sanatocin Kudancin Kasar irin su Godwsill Akpabio sun sa baki game da lamarin. Ga dai Sanatocin Yankin Arewa da su ka koka da abin da ke faruwa kuma su ka nemi a dauki mataki:

1. Rabiu Kwankwaso

A zaman da aka yi jiya Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Kwankwasoyayi tir da barnar da ake yi a Yankin ya kuma nemi Jami’an tsaro su yi bakin kokari domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar.

2. Barau Jibrin

Shi ma Sanatan Kano ta Arewa watau Barau Jibrin yayi Allah-wadai da ta’adin da aka jawo a irin su Benuwe ya kuma ce Jami’an tsaro ba su abin da ya dace shi ma yana mai kira a tsaida wannan mummunan kashe-kashe.

KU KARANTA: Ikon Allah: An yi garkuwa da wani jariri a Najeriya

3. Garba Binta

Sanata Masi Garba ta Adamawa ta nemi a hada karfi-da-karfe a ajiye duk wani banbanci a maganar tsaro. Sanatan wanda ita kadai ce mace daga Arewacin Kasar tace Jihohi da yawa sun yi kan iyaka ne da wasu kasashe kuma ya kamata a duba masu shigowa cikin wannan Jihohi.

4. Jeremiah Useini

Sanatan Filato Useini shi ma ya nemi a kawo karshen rikicin ya kuma ce a matsawa Jami’an tsaro su yi aikin da ya dace ko kuma a kori duk wanda aka samu da yin ba dai-dai, yace idan ba haka ba, ba za a ga karshen rikicin ba.

5. Bukola Saraki

A karshe Shugaban Majalisar Dattawan bayan yayi magana da tsohon Gwamnan Benuwe Gabriel Suswam ya yanke shawarar cewa za a gayyaci IG na ‘Yan Sanda ya zo yayi bayani game da rikicin Benuwe da sauran Yankin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel