Sojoji 22 suka rasa rayukansu, 75 kuma suma suka samu rauni a kokarin yakar Boko Haram

Sojoji 22 suka rasa rayukansu, 75 kuma suma suka samu rauni a kokarin yakar Boko Haram

- Babban kwamandan kungiyar sojoji ta MNJTF Manjo Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa sojoji 22 ne suka rasa rayukansu sai kuma 75 suka samu raunuka a wurin yakar kungiyar Boko Haram

- Manjo Janar Lucky Irabor yace a kalla ‘yan ta’adda 59 ne aka kashe a wurin fadan, sai kuma 5 da aka kama sannan sai masu kunar bakin wake 3 da aka kashe

- Kanal Timothy Antigha, babban jami’in sojojin mai kula da harkokin jama’a na kungiyar MNJTF ya bayyana cewa cikin abubuwan da aka samu daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da motoci 3 sai kuma bamabamai

Babban kwamandan kungiyar sojoji ta MNJTF Manjo Janar Lucky Irabor, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa sojoji 22 ne suka rasa rayukansu sai kuma 75 suka samu raunuka a wurin yakar kungiyar Boko Haram a lokuta daban daban, don magance ta’addanci a yankin Chad N’Djamena.

Manjo Janar Lucky Irabor yace a kalla ‘yan ta’adda 59 ne aka kashe a wurin fadan, sai kuma 5 da aka kama sannan sai masu kunar bakin wake 3 da aka kashe, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sojoji 22 suka rasa rayukansu, 75 kuma suma suka samu rauni a kokarin yakar Boko Haram
Sojoji 22 suka rasa rayukansu, 75 kuma suma suka samu rauni a kokarin yakar Boko Haram

Kanal Timothy Antigha, babban jami’in sojojin mai kula da harkokin jama’a na kungiyar MNJTF ya bayyana cewa cikin abubuwan da aka samu daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da motoci 3 sai kuma bamabamai.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga a majalisa akan jirgin $496m da Buhari ya siyo

Antigha ya bayyana cewa yankunan garuruwan Gashigar, Arege da Metele, an magance matsalar ‘yan ta’addan dake damunsu a wuraren.

A halin da ake ciki Shugaban majalisa Bukola Saraki a zaman majalisar na ranar Laraba, ya karanto takardar da shugaba Buhari ya rubutawa majalisar ta neman amincewarsu game da cire $496m daga asusun ribar kudin danyen mai, don siyen jirgin Sojoji.

Buhari ya bayyan a cikin takardar cewa kudin har an ciresu daga asusun an biya kasar Amurka kudin jiragen 12 kafin amincewar majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel