A dakatar da Kashe-Kashen jihar Benuwe - Shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga shugaba Buhari

A dakatar da Kashe-Kashen jihar Benuwe - Shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga shugaba Buhari

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya tashi ya farga wajen dakatar da kashe-kashen da zubar da jini a jihar Benuwe wanda ke kara ta'azzara a kullum.

A ranar Larabar da ta gabata ne Secondus ya kirayi shugaba Buhari da cewar muddin ba a kawo karshen wannan zubar da jini ba to kuwa akwai yiwuwar habakar sa zuwa rikici na kasa baki daya.

A dakatar da Kashe-Kashen jihar Benuwe - Shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga shugaba Buhari
A dakatar da Kashe-Kashen jihar Benuwe - Shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga shugaba Buhari

Wannan kira ya fito ne da sanadin mai magana da yawun shugaban jam'iyyar, Ike Abonyi, inda ya bayyana cewa yawan kashe-kashe a jihar Benuwe da sauran bangarorin kasar nan ka iya janyo koma baya mai matukar muni a kasar nan.

KARANTA KUMA: 'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga da gawar mabiyin su da jami'an 'Yan Sanda suka harbe a garin Abuja

Legit.ng ta ruwaito cewa, ta kowane bangare na mahanga akan wannan kashe-kashe dake ci gaba da ta'azzara a kasar nan, za ka ga cewar ba bi wani abu da yake haifarwa face koma bayan zamantakewa da kuma tattalin arziki kamar yadda shugaban jam'iyyar ya bayyana.

Ya kara da cewa, Najeriya da sauran kasashen duniya su na ci gaba da zuba idanu a yayin da romon dimokuradiyya da ya kamata su kwankwada ke ci gaba da zagwanyewa sakamakon rashin kulawar gwamnatin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel