Yansanda sun damko wuyar yan bindiga 11 da suka bindige mutane 5 a jihar Kebbi

Yansanda sun damko wuyar yan bindiga 11 da suka bindige mutane 5 a jihar Kebbi

Akalla mutane guda biyar ne suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga a garin Bena, cikin karamar hukumar Danko-Wasagu na jihar Kebbi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan Yansandan jihar, Kabiru Ibrahim ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labaru, inda yace wasu yan bindigan su 11 da suka hallaka mutanen sun fada komar Yansanda, ya kara da cewa guda 10 daga cikinsu yan jihar Zamfara ne, 1 kuma daga Kebbi.

KU KARANTA: Jama’an jihar Bauchi sun kammala shirin tarbar Buhari a ranar Alhamis

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishina Ibrahim yana cewa yan bindigar sun kai harin Bena ne bayan kimanin kwanaki biyu da suka kai kwatankwacin harin a kauyen Kaboro, dake tsakanin Zamfara da Kebbi.

Ya bayyana sunayen yan bindigar kamar haka: Lawal Ibrahim, Nasiru Lawali, Yahaya Mohammed, Haliru Shantali, Hussaini Hamisu, Mohammed Nuhu, Habibu Sani, Rilwanu Mohammed, Mohammed Sanusi, Mohammed Bara’u da Abubakar Haruna.

Daga karshe yace hukumar Yansandan jihar ta aika da Yansandan masu kwantar da tarzoma, jami’an SARS, Yansandan kan hanya da kuma jami’an leken asiri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel