Kiwon lafiya: Masana sun gano cewa ashe cin kayan kwalama na janyo ciwon gabobi

Kiwon lafiya: Masana sun gano cewa ashe cin kayan kwalama na janyo ciwon gabobi

Wata sabuwar bincike da masana kimiyyan lafiya suka gudanar ya bayyana cewa fiye cin kayan soye-soye da abincin gwamgwani suna kara tsananta ciwon amosanin gabbai da gabobi.

Wannan binciken ya fito ne daga Jami'ar Kiyon lafiya na Rochester, idan suka ce kwayoyin hallita 'bacteria' dake cikin hanji suna da alaka da janyo kumburi da yake haifar da zafi a cikin kasusuwa na mutane masu kiba ba marasa kiba ba.

Kiwon lafiya: Masana sun gano cewa ashe cin kayan kwalama na janyo ciwon gabobi
Kiwon lafiya: Masana sun gano cewa ashe cin kayan kwalama na janyo ciwon gabobi

Sabon binciken ya nuna cewa daidaita adadin kwayoyin hallitar da ke cikin haji ta hanyar amfani da ababen dake taimakawa wa kwayoyin hallita hayayafa a turence 'Probiotic' ya kawar da alamun rashin lafiyan a jikin beraye da ake gwaji da su.

DUBA WANNAN: Wani limami 'dan Najeriya ya tsinci kudi mai yawa a Saudiyya, ya mayar dasu saboda tsoron Allah

A baya, masana sunyi tsamanin cewa takura wa gabobin jiki ne ke haifar da cutar ta amosanin gabbai wadda a turance ake kira da "Osteoarthritis " kuma ana tunanin rage kiba zai sanya a samu sauki.

Jagoran binciken Farfesa Michael Zuscik yace "guringuntsi ya kasance mai laushi da kuma maiko, wanda ke taimakawa gwiwa wajen motsawa yayinda ka rasa hakan gurin zai zamo kashi ne akan kashi, dutse da dutse, wannan shine makura sai dai a canja kashin gwiwar.

Abinda muke kokarin samowa yanzu shine yanda za'a kare faruwar hakan.

Masu binciken sun bawa bera abinci me gina jiki kamar "cheeseburger da milkshake" bayan sati beran yayi kiba sannan ya kamu da ciwon siga. Ya ninka beran da aka ciyar da abinci mai gina jiki saffa-saffa sau biyu.

Masu binciken sun tsara ci gaba da wannan gwajin a jikin mutane, suna fatan kwantata mutune masu nisan shekaru wanda suke da ciwon gabobin da kuma wanda basu dauke da cutar domin gano alakar dake tsakanin kwayoyin halitar da ke hanjin da gabobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel