Dakarun sojoji sun kama manyan yan fashi a jihar Kogi

Dakarun sojoji sun kama manyan yan fashi a jihar Kogi

Dakarun sojoji tare da na TOTAL FREEDOM sun yi arangama da wasu yan fashi dake addaban kauyukan Kpanche, Bereko da kuma Ozugbe na karam ar hukumar Bassa dake jihar Kogi a yayinda suke gudanar da aiki.

An kama shida daga cikin yan fashin yayinda sauran suka gudu sakamakon wutan da sojojin suka buda masu.

Sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigogi, mujalla da kuma harsasai.

Dakarun sojoji sun kama manyan yan fashi a jihar Kogi
Dakarun sojoji sun kama manyan yan fashi a jihar Kogi

Sun kuma ba mazauna yankin dake zaman dar-dar tabbacin samun kariya sannan sun shawarce su da kada su ji tsoro a maimakon haka sun sanar da duk wani ayyuka ko motsi da basu gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Akalla masu bauta 7 ne suka mutu sannan goma sha biyu suka jikkata a yayinda yan kunar bakin wake suka kai hari wani masallacin Bama a safiyar Lahadi, inji wata majiya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama Sanata Melaye a filin jirgin sama

Majiya daga hukumar bayar da agajin gaggawa tace a yanzu haka wadanda suka ji rauni na samun kulawar likita a asibitin Bama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel