Za’a kashe dala miliyan 322 daga kudin da Abacha ya sata akan talakawa da gajiyayyu

Za’a kashe dala miliyan 322 daga kudin da Abacha ya sata akan talakawa da gajiyayyu

Gwamnatin tarayya ta bakin ministan kudi, Kemi Adeosun ta sanar da yadda zata kashe dala miliyan 322 na kudaden da tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, janar Sani Abacha ya zaftara.

Jaidar The Cables ta ruwaito Minsitan tana cewa gwamnati ta himmatu wajen kashe makudan kudaden ne don amfanin tarin talakawan Najeriya, gajiyayyu da marasa karfi daka cikin al’umma.

KU KARANTA: Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Kemi ta bayyana haka ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Afrilu a birnin Washington na kasar Amurka, yayin da ganawa da yan jaridu, tare da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emeifel, inda tace a yanzu haka kudaden na jibge a asusun babban bankin Najeriya.

“Manufar shirye shiryen gwamnati na tallafa ma talakawan Najeriya shine don samar da bashi da kuma tallafi ga gajiyayyu da marasa karfi dake cikin al’umma. Zamu cigaba da toshe duk wasu ramuka da ake sace kudi a hukumar NNPC.” Inji ta.

Kemi ta cigaba da cew: “Kun tuna lokacin da Sunusi yace an saci dala biliyan 20 daga NNPC? Ai da ba karamin abu zamu cimmawa ba da ace mun samu dala biliyan 20 kwance a asusun kasa."

Da take karin haske game da cigaban tattalin arziki da aka samu, Kemi ta bada tabbacin cigaban da za’a samu a shekarar 2019 sai yafi na shekarun baya, amma ta bukaci dukkan bangaorin da abin ya shafa su jajirce.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel