Auren jinsi: Buhari ya mayar wa da Firaministar Ingila martani

Auren jinsi: Buhari ya mayar wa da Firaministar Ingila martani

- Shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila inda ya halarci taron kasashen kungiyar common wealth

- Firaministar kasar Ingila, Theresa May, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta halasta auren jinsi ga masu sha'awar hakan

- Majalisar dattijai tayi doka ga duk wanda aka samu na nuna soyayya ga irin jinsin sa

A jiya ne shugaba Buhari ya dawo daga birnin Landon inda ya halarci taron kasashen kungiyar common wealth.

Shugaba Buhari ya isa kasar Ingila gabanin taron domin gudanar da wasu uzuri da ba a bayyana yanayin su ba.

Auren jinsi: Buhari ya mayar wa da Firaministar Ingila martani
Buhari da Firaministar Ingila Theresa May

Firaministar kasar Ingila, Theresa May, a wata ganawa da tayi da shugaba Buhari, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta bawa masu son yin auren jinsi dama, ta hanyar canja dokokin da majalisar kasa tayi a kan duk wadanda aka samu na aikata hakan.

DUBA WANNAN: Kalli yadda mummunar gobara ta mayar da kasuwar Hausawa ta Mile 12 a Legas

A martanin sa, shugaba Buhari, ya shaidawa Firaministar cewar, batun auren baya cikin al'adar mutanen Najeriya kuma ba kalubale ne dame yiwa Najeriya wata barazana ba.

"Auren jinsi baya cikin al'adar mutanen Najeriya kuma batun auren jinsi ba barazana ba ce ga tsaro ko zaman lafiya a Najeriya ba.

Babban kalubalen mu a Najeriya shine matsalolin tsaro da cin hanci," a kalaman shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel