Rundunar Sojin kasa ta damke wasu 'yan Kungiyar Asiri 23 da 15 masu Fashe Bututun mai a jihar Legas

Rundunar Sojin kasa ta damke wasu 'yan Kungiyar Asiri 23 da 15 masu Fashe Bututun mai a jihar Legas

A ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar Sojin kasa ta Najeriya ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke wasu mutane 23 da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a yayin da sake gudanar horaswa gami da tantance sabbin masu shiga 'yan kungiyar.

Rundunar Sojin ta kuma bayyana cewa ta samu nasarar cafke wasu mutane 15 da ake zargin su da Fashe Bututun mai inda aka damke su tare da jarkoki 31 na tataccen man fetur.

Rundunar Sojin kasa ta damke wasu 'yan Kungiyar Asiri 23 da 15 masu Fashe Bututun mai a jihar Legas

Rundunar Sojin kasa ta damke wasu 'yan Kungiyar Asiri 23 da 15 masu Fashe Bututun mai a jihar Legas

Manjo Janar Enobong Udoh, Kwamandan dakarun sojin kasan dake bataliya mai lamba 174 a yankin Ikorodu na jihar Legas shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai.

KARANTA KUMA: Gwamnati ta tarwatsa wasu Gidajen sayar da Barasa da na Karuwai a jihar Jigawa

Udoh wanda Janar Moundhey Ali ya wakilta a yayin wannan sanarwa ya bayyana cewa, an yi nasarar cafke miyagun ne a lokuta daban-daban sakamakon leken asiri da kuma tattaro bayanai na sirri.

NAIJ.com ta fahimci cewa, rundunar Sojin ta cafke masu kishi da zaman lafiya na kasar nan ne a yankunan jihar Legas tun a ranar 16 ga watan Afrilu da kuma wasu a sassa na jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel