Bidoyon Kamfen din PDP na 2015 inda Jonathan ke yabon samari ya dawo sama a dandulan sada zumunta

Bidoyon Kamfen din PDP na 2015 inda Jonathan ke yabon samari ya dawo sama a dandulan sada zumunta

- Shugaba Buhari ya kwapsa kan batun lalacin samari

- Gwamnatinsa ta kare shi, kan cewa ba'a fahimceshi bane

- Da gaske wasu na lalaci, amma mafi yawa nem an na kai suke

Bidoyon Kamfen din PDP na 2015 inda Jonathan ke yabon samari ya dawo sama a dandulan sada zumunta
Bidoyon Kamfen din PDP na 2015 inda Jonathan ke yabon samari ya dawo sama a dandulan sada zumunta

In dai ba'a yabi saurayi da budurwa a kasar nan ba, ba'a fallashe shi ba, domin matasa sune suke bada muhimmiyar gudummawa kan dora kowacce gwamnati, musamman wannan wadda tazo ba ko sisinta taci zabe da kokarisamari.

Ababen more rayuwa sunyi wa talaka nisa, don haka sai ya hakura, ya koma neman iya wanda ko a yau aka ci an gode. Samari rututu ba jari ba aiki, ba ilimi isasshe babu tallafi, sai ma cire shi kamar ba'a tausayinsu.

A lokacin da jam'iyyar PDP mai adawa takemulki, an tafka uwar sata, amma kuma an baiwa samari jari, an taimaka wa masu neman na kansu, ba'a tsangwame su ba, kuma an musu daidai yadda dai babu fallasa.

DUBA WANNAN: Ministar kudi ta kare kanta kan batun N10b na motocin majalisu

Amma tun zuwan wannan gwamnati, sai cire tallafi kawai da korar jama'a da cewa suje su nema wa kansu na kansu, bayan ababen rayuwar sunyi tsada, babu gidajen, babu kudin haya, babu ko kudin jari, babu aikin yi, yawanci kuma ba yin kansu bane.

A bidiyo da yanzu ake ta yayatawa a yanar gizo, sai ga tsohon shugaba Jonathan yana yabon kwazo da dagiyar samarin Najeriya, hakkakewarsu koda a yanayin babu, neman na kai da iya hobbasa. Bidoyon an nade shi ne lokacin Kamfe na 2015.

Ya tunatar da yadda ya bayar da jari, da sukolaship ga masu kokari, da ma dakikai. Ya fadi yadda yake sa rai samarin zasu ceto Najeriya daga matsalar da manyan kasar nan suka jefa ta tun bayann samun 'yancin kai.

Shi kuwa Janar Buhari, sai ga nasa bidiyo a taron duniya, yana cewa da yawan samarin Najeriya malalata ne, basu da katabus sai son zaman kashe wando, da ma cima zaune, da jiran a basu daga kudin mai, bayanai da suka harzuka matasa.

A hawansa dai, shugaba Buhari yace a koma gona, ya rufe iyakoki inda akan shigo da kayan abinci, gwanjo, da ma motocin sayarwa, inda ake harbe masu fasa-kwabri.

Ya kuma cire dukkan tallafin man fetur, man ya koma N145, a lita daya, ya ce duk cuwa-cuwa ce. Sai kuma gashi wai ana kashe tiriliyan daya da rabi kan tallafin man a duk shekara, koda yake man yayi dan tsada a duniya.

Babu dai wani aikin kuzo-ku-gani da gwamnatin tayi wanda a iya cewa dubbai sun samu, babu wani jari kamar na waccan gwamnatin, sai ma 'ya'yan manya da aka dauka a manyan ofisoshi daga hawansa.

Farashin dala ya ninninka daga 198 a PDP zuwa akalla 500 a bara biyu, kafin ya sauko ya daidaita a 350, wanda hakan ya haifar da uwar yunwa, talauci da hauhawar farashi da ma saurin kamuwa da cututtuka tunda ba'a koshi ba.

Duka da a iya cewa wannan burbushin tsiyar PDP ce, dole a baiwa gwamnatin APC laifin inda ta hana dala ta kuma hana duk wani motsi da kudi, da sunan .haramun'.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel