Shehi Ɗahiru Bauchi ya nemi Gwamnatin tarayya akan ta saukaka wahalar Talaka a Najeriya

Shehi Ɗahiru Bauchi ya nemi Gwamnatin tarayya akan ta saukaka wahalar Talaka a Najeriya

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, jagoran 'darikar Tijjaniyya na Najeriya Shehi Ɗahiru Usman Bauchi, ya nemi gwamnati tarayya akan ta samar da hanyoyi na saukaka tagayyarar takalawan kasar nan.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a jihar Bauchi dangane da kammala bikin Maulidin Shehi Ibrahim Inyass da aka gudanar a biranen Abuja da Kaduna a makon da ya shude.

Babban jagoran yana mika kokon barar sa ga gwamnatin tarayya domin ta kaddamar da manufofi da kuma shirye-shirye da za su inganta yanayin zamantakewa da tattalin arziki a kasar nan.

Shehin na Bauchi ya kuma kirayi masu hannu da shuni wajen taimakon matalauta ta hanyoyin da za su samu sauki na kangin talauci da suke ciki, yayin da kuma ya tunatar da 'yan siyasar kasar nan akan su tabbatar da masu jefa masu kuri'u sun sharbi romo na dimokuradiyya.

Shehi Ɗahiru Bauchi ya nemi Gwamnatin tarayya akan ta saukaka wahalar Talaka a Najeriya
Shehi Ɗahiru Bauchi ya nemi Gwamnatin tarayya akan ta saukaka wahalar Talaka a Najeriya

Ya kuma jajintawa 'yan uwan wadanda suka rasa rayukan su da kuma wadanda suka raunata a yayin bikin Maulidin a sakamakon dandazo da cinkoson dumbin masoya Shehi Inyass.

KARANTA KUMA: Hotunan Shugaba Buhari da Uwargidan sa a yayin wata liyafa a fadar Sarauniyar Ingila

Jagoran na Tijjaniyya ya kuma yiwa kasar nan addu'o'i na ganin karshen nau'ikan ta'addanci da suka hadar da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma rikita-rikitar hare-hare da ta addabi mafi akasar sassan kasar nan.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Shehin Malamin ya gargadi al'ummar kasar nan dangane da jefa kuri'un su ga 'yan takara nagari da kuma mallakar katin zabe sakamakon zaben 2019 da yake karatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel