Zaben 2019: An soma zanga-zangar neman Buhari ya janye kudurin sa na tazarce a birnin Landan

Zaben 2019: An soma zanga-zangar neman Buhari ya janye kudurin sa na tazarce a birnin Landan

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da labarin cewa wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun soma yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga suna bukatar ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar da ya ayyana a zaben 2019 mai zuwa.

Sai dai daya daga cikin hadiman na shugaban kasa ya bayyana cewa wannan ba abunda yake nunawa sai tabbacin cewa shugaban kasar na kokarin dora kasar bisa turbar da ta dace ne shiyasa hakan ke ta faruwa.

Zaben 2019: An soma zanga-zangar neman Buhari ya janye kudurin sa na tazarce a birnin Landan

Zaben 2019: An soma zanga-zangar neman Buhari ya janye kudurin sa na tazarce a birnin Landan

KU KARANTA: Lokuta 6 da aka taba sace sandar girma a majalisar Najeriya

NAIJ.com ta samu cewa wannan hadimin na shugaban kasa ya kara da cewa haka zalika duba da yadda gwamnatin shugaba Buhari din ke ta kokarin yaki da cin hanci da rashawa, hakan ya sanya dole wasu jiga-jigan barayin gwamnati suka shiga tashin hankali.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotu dake a unguwar Maitama a garin Abuja, babban birnin tarayya ta bayar da umurmi ga jami'an tsaron Najeriya da suka hada da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron farin kaya watau SSS da kar su kuskura su kama Satana Ovie Omo-Agege daga jihar Delta.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya biyo bayan bukatar Lauyan Sanatan mai suna Aliyu Umar ya roki kotun a cikin karar da ya shigar a gaban ta .

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yaki da ta'addanci: Soji sunyi halaka 'yan ta'addan makiyaya 21 a Benue

Yaki da ta'addanci: Soji sunyi ragargaji 'yan ta'addan makiyaya a Benue

Yaki da ta'addanci: Soji sunyi ragargaji 'yan ta'addan makiyaya a Benue
NAIJ.com
Mailfire view pixel