An karawa Jami’an tsaron da su ka damko Evans karin girma a wajen aiki

An karawa Jami’an tsaron da su ka damko Evans karin girma a wajen aiki

- An karawa yaran Abba Kyari matsayi a Rundunar ‘Yan Sanda

- Abba Kyari ya yabawa Sufetan ‘Yan Sanda na kasar da kokari

- Kwanakin baya ma an damke wasu masu garkuwa da jama’a

Sai bayan watanni 10 da damke rikakken tsageran nan da ake zargi da garkuwa da mutane watau Evans sannan Sufetan 'Yan Sanda Ibrahim Idris ya yi wa Jami’an da su ka kama shi karin girma kamar yadda mu ka samu labari.

An karawa Jami’an tsaron da su ka damko Evans karin girma a wajen aiki
Abba Kyari ya zama DCP na 'Yan Sanda a shekara 43

Babban Jami’in ‘Yan Sanda watau Abba Kyari shi ne yayi yadda yayi ya kama Evans bayan shekaru 5 yana bin sawun sa a Najeriya. Yanzu Kyari mai shekaru 43 shi ne ‘Dan autan Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a kasar.

KU KARANTA: An kama wani babban 'Dan bindiga a Jihar Taraba

Kyari yayi nasarar karbe katafarun gidaje 7 da kuma motoci da gwala-gwalai da sarkoki masu tsada da manyan makamai daga hannun Evans. Evans dai ya saye wadannan kaya ne duk da haramtaciyyar sana’ar da yake yi.

A baran da aka yi ram da Evans an kuma cafke manyan mukarraban sa fiye da 20 wanda daga cikin har da Jami’an tsaro guda 2. Yanzu dai an karawa ‘Yan Sanda 45 da su ka mikawa Hukuma Evans din matsayi a wurin aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel