Maryam Sanda ta nemi mijin ta ya sake ta kafin mutuwar sa - Inji Mashaidi

Maryam Sanda ta nemi mijin ta ya sake ta kafin mutuwar sa - Inji Mashaidi

A ranar Alhamis 19 ga watan Afrilu, babbar kotun birnin tarayya dake zamanta a unguwar Jabi ta ci gaba da sauraron kara tare da gudanar da shari'ar matar nan da ake zargin ta da kashe mijin ta Bilyaminu, watau Maryam Sanda.

Kotun ta samu wani karin haske dangane da yadda lamarin ya kasance kafin mutuwar Bilyaminu Bello, inda wani mashaidin masu karar Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa, Maryam ta nemi mijin ta ya sawwake mata tun kafin mutuwar sa.

Mashaidin wannan shari'a Ibrahim ya shaidawa kotun cewa, ya kasance a gidan abokin sa Marigayi Bilyamu a yayin da suke rage lokaci har wajen karfe 8.00 na daren ranar da mai aukuwar ta afku.

Maryam Sanda ta nemi mijin ta ya sake ta kafin mutuwar sa - Inji Mashaidi
Maryam Sanda ta nemi mijin ta ya sake ta kafin mutuwar sa - Inji Mashaidi

A yayin da suke hirar su ta yau da kullum, kwatsam sai Maryam ta nemi ganawa da mijinta inda mai masu hidimar gida Sadiya ta zo kiranshi. A sanadiyar haka ne Bilyaminu ya tafi domin biyan bukatar kira na matar sa.

Jim kadan bayan tafiyar Bilyaminu sai hayaniya ta fara tashi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana, inda abokin sa Ibrahim ya bi sahun marigayi domin jin ba'asi.

Isar sa ke da wuya ya riske su cukwikwiye da rigunan juna, inda Maryam ta ke tayar da jijiyar wuya akan sai mijin ta ya sawwake ma ta.

KARANTA KUMA: 'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

Ana tsaka da wannan rikici ne Maryam ta fashe wata kwalba kuma ta nufaci sheke mijin nata nan take, inda wani dan uwa ga ma'auratan Usman Aliyu, ya shawarce Ibrahim akan ya kyale su domin gudun jin kunya ta shiga tsakanin al'amarin miji da matar sa.

Bayan faruwar hakan ke da wuya, sai Abba Bello wani dan uwa ga marigayi Bilyaminu ya kiraye shi ta wayar salula inda ya labarta masa wannan mummunan batu na mutuwar aminin sa, wanda isar sa asibitin Maitama ke da wuya ya yi kacibus da gawar sa.

Ibrahim dai ya bayyana kotun cewa ko kadan ba ya da masaniyar sanadin mutuwar Bilyaminu domin kuwa tuni ya bar gidan ya kama gaban sa bayan daukar shawara da yayi.

Alkali Yusuf Halilu, ya sake daga sauraron karar zuwa ranakun 15 da 16 na watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel