Hukumar sojin Najeriya tayi gargadi na musamman ga 'yan siyasa

Hukumar sojin Najeriya tayi gargadi na musamman ga 'yan siyasa

- Hukumar Sojin Najeriya ta gargadi yan siyasa su dena amfani da sojoji wajen cinma burinsu

- Hukumar sojin ta zargi wasu yan siyasa a jihar Taraba da batawa soji suna a idanun al'umma

- Hakan kuma ya janyo al'ummar jihar na Taraba suka ki bayar da hadin kai yayin da sojojin ke gudanar da ayyukan samar da tsaro

Hedkwatan tsaro na Najeriya ta gargadi yan siyasa su guji yin amfani da harkokin tsaron kasa da sojojin Najeriya wajen cinma burinsu na siyasa. Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin direktan sadarwa na hukumar, Brig. Janar John Agim, yayinda yake yiwa manema labarai jawabi jiya a Abuja.

Hukumar sojin Najeriya tayi gargadi na musamman ga 'yan siyasa
Hukumar sojin Najeriya tayi gargadi na musamman ga 'yan siyasa

DUBA WANNAN: Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P naira 5.7bn

Agim yace irin wannan halin yana kashe wa sojojin gwiwa wanda hakan ba zai haifar da alheri ga al'ummar Najeriya ba. "Soji ne kashin bayan kowane kasa, har ma da Najeriya, idan muna kashe musu gwiwa, abokan gabansu zasu samu galaba a kansu kuma sauran yan kasa zasu shiga cikin fitina."

Agim yayi korafi a kan yadda wasu yan siyasa ke kokarin shafawa soji kashi a idanun al'umma, musamman a jihar Taraba inda sojojin ke gudanar ta atisayen Ayem Akpatuma kuma hakan ya janyo sojojin basu samu cikaken hadin kan al'umma ba.

"Misali, shugaban karamar hukumar Takum bai bawa Bataliya 93 hadin kai ba, maimakon hakan sai ya bata musu suna a wajen al'umman mazauna yankin.

"Abubuwan daya aikata kafin fara aikin, da kuma lokacin da ake gudanar da aikin sun nuna karara cewa yana adawa da sojojin ne kuma a lokuta da yawa hakan yasa al'umma sun juya wa sojojin baya."

Ya kuma bayar da sanarwan cewa Sojin ta kara wa'adin atisayen har zuwa 14 ga watan Mayun 2018 saboda halin rashin tsaro da ke adabar jihar.

Agim ya kuma ce sojoji guda 13 sun rasu, kuma wasu 7 sun sami raunuka yayinda suke gudanar da aikin samar da tsaro a jihar ta Taraba. Kazalika, an bannata wasu daga cikin kayayakin aiki su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel