An jefa wani na hannun daman Buhari a kurkuku kan zargin zambar N182m

An jefa wani na hannun daman Buhari a kurkuku kan zargin zambar N182m

Wata babban kotun tarayya dake garin Ilorin ta tsare Dr. Saadu Alanamu a kurkuku kan zargin zambar kudi kimaanin naira miliyan 182 da kuma sabawa ka’idar beli.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan Alamu ga majalisar dattawa a makon da ya gabata domin a tabbatar da shi a matsayin kwamishinan hukumar kidaya ta kasa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a shekarar da ya gabata an zabi Alamu cikin hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da sauran hukumomi da mukaddashin shugaban kasa a wannan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar duk da cewar wannan hukuma na bincike akansa.

An jefa wani na hannun daman Buhari a kurkuku kan zargin zambar N182m

An jefa wani na hannun daman Buhari a kurkuku kan zargin zambar N182m

Sai dai bayan koke-koken jama’a, Osinbajon ya cire sunansa inda daga bisani hukumar ICPC ta kama shi tare da gurfanar das hi akan zamba.

KU KARANTA KUMA: Kokarin juyin mulki ne ya sa aka kai harin jiya na majalisa - Inji Shehu Sani

Ana tuhumar Alamu wanda ya kasance shugaban kungiyar jigajigan makarantar poly na jihar Kwara, tare da babban Daraktan Namylas Nigeria Limited, Salman Sulaiman, kan zargin amsan cin hanci daga wani mai aikin kwangila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Aka ce basa ji: Sojoji sun yi luguden wutar azaba akan mayakan Boko Haram (Bidiyo)

Aka ce basa ji: Sojoji sun yi luguden wutar azaba akan mayakan Boko Haram (Bidiyo)
NAIJ.com
Mailfire view pixel