An kashe maciji ba’a sare kansa ba: Yaran Buharin Daji sun hallaka wasu mutane 2 a jihar Zamfara

An kashe maciji ba’a sare kansa ba: Yaran Buharin Daji sun hallaka wasu mutane 2 a jihar Zamfara

Wasu yan bindiga da ake zargin yaran tsohon kasurgumin dan fashin nan ne da ya addabi jihar Zamfara, Buharin Daji sun bindige wasu mutane guda biyu har lahira ba cas ba as, inji rahoton Rariya.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yan bindigan sun yi ma mutanen kisar gillar ne yayin da suke kan hanyar kauyen Kabaro dake tsakanin garin Bena da Dansadau, duk a cikin karamar hukumar Maru ta jihar.

KU KARANTA: Hargitsi a majalisar dattawa: Jami’an Yansanda sun kwato ‘Sandar Iko’ da ɓarayi suka sace

Rahotanni sun tabbatar da cewar maharani sun hallaka wani mai suna Abdullahi mai kifi ne ta hanyar bindige shi, sa’annan suka yi masa yankan rago, daga bisan kuma suka isahe Malam Shehu Badakkare, inda suke murde masa wuya sakamakon kasa kashe shi da bindiga.

Sai da majiyar ta ruwaito zuwa yanzu an yi ma mamatan jana’iza a babban asibitin garin Dansandau. Tsaro ya kara tabarbarewa a Zamfara tun bayan kisan Buharin Daji da wani tsohon Yaronsa yayi.

Inda ko a kwanakin baya sai da yaran Buharin suka shiga jihar Kaduna, inda suka bindige wasu Sojoji guda goma sha daya dake jibge a wani kauyen Birnin Gwari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An yi ca a kan Gwamnatin Buhari ta saki ‘Dan Jaridar da aka kama

An yi ca a kan Gwamnatin Buhari ta saki ‘Dan Jaridar da aka kama

Tsare ‘Dan Jarida: Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Sandan Najeriya da babbar murya
NAIJ.com
Mailfire view pixel