Ilimin addinin musulunci ba koma baya bane, haka kuma musulmai ba jahilai bane - Sarkin Musulmai

Ilimin addinin musulunci ba koma baya bane, haka kuma musulmai ba jahilai bane - Sarkin Musulmai

- A kokarin kare martabar addinin musulunci da Sarkin musulmi na sokoto Alhaji sa'ad Abubakar yake. Yace duk wani musulmi ba jahili bane sannan addinin musulunci bai zamo koma baya ba

Ilimin addinin musulunci ba koma baya bane, haka kuma musulmai ba jahilai bane - Sarkin Musulmai
Ilimin addinin musulunci ba koma baya bane, haka kuma musulmai ba jahilai bane - Sarkin Musulmai

Sarkin musulmi na sokoto Alhaji sa'ad Abubakar ya fada a kokarin kare martabar addinin musulunci. Yace duk wani musulmi ba jahili bane sannan addinin musulunci bai zamo koma baya ba.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta karyata jita - jitar kai harin 'Yan Shi'a Abuja

Sultan din ya fara da bayyana sabanin da aka samu daga wajen mutane dangane da ilimin addini yace abu ne mai kyau domin bai kasance abin gujewa ba. Yayi jawabin nasa ne a ranar litinin 16 ga wannan wata a taron taya murnar Sheik Adam Al-Elory shekaru 100 wanda aka gudanra a jihar Legas.

Majiyarmu Legit.ng Ta bayyana cewa sultan din yayi kira ga musulmi dasu jajirce wajen bayyana duniya cewar su ba jahilai bane.

Ya fara da cewa" bazamubar mutane suna kaskantar damu ba suna cewa bamu da amfani. Ya kamata muyi duba izuwa ga wannan batu, sannan mu tambayi kawunan mu meyasa mutane suke mana kallon marasa ilimi? Ta yaya za'a kira mutumin daya haddace alqurani ya kuma karantashi da jahili dan kawai bai iya turanci ba..

Al-Elory mashahurin malamin addini ne sannan kuma shine wanda ya kafa Markaz a Agege wato cibiyar ilimin addinin musulunci dake legos ya rasu a shekarar 1992.

A halin yanzu NAIJ. com ta bayyana mana cewa sultan din sokoto kuma jagora na (NSCIA) ya koka dangane da matsalar saka hijab sannan ya bada shawarar mata su cigaba da kokarin sakawa.

Yace a nasa bangaren hijabi wata sutura ce ga dukkan wata 'ya mace sannan kuma wani yanki ne daga addinin musulunci. Me yasa maganar hijabi take kawo cece kuce wanda har ya kawo ga matan musulmi ke kawata adon su wanda hakan ya kasance abun ki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel