Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama manyan barayin nan da suka addabi jihar

Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama manyan barayin nan da suka addabi jihar

- A kokarin da hukumomin tsaro suke na kawar da ayyukan ta'addanci a kasar nan, dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama wasu manyan masu laifi da suka hada masu garkuwa da mutane, barayin shanu, masu fyade, barayin motoci, da kuma wadanda suka mallaki bindigogi ba a bisa ka'ida ba

Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama manyan barayin nan da suka addabi jihar
Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama manyan barayin nan da suka addabi jihar

A kokarin da hukumomin tsaro suke na kawar da ayyukan ta'addanci a kasar nan, dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama wasu manyan masu laifi da suka hada masu garkuwa da mutane, barayin shanu, masu fyade, barayin motoci, da kuma wadanda suka mallaki bindigogi ba a bisa ka'ida ba.

DUBA WANNAN: Wata kungiyar musulmi, na so a sake canja fasalin Naira dari, ji dalilinsu

Rundunar tace ta samu nasarar kama wadanda ake thuhumar ne a wani samame data gudanar a kananan hukumomin, Tafa, Suleja, da Mashegu inda suka kama kimanin mutum 19 dauke da makamai, kamar yanda kakakin rundunar na jihar Neja Abubakar Dan Inna, ya sanar.

Daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Ali Muhammad dan garin Sawmil a karamar hukumar Mokwa da Isiya Hassan dan kauyen Bodiga a karamar hukumar Mashegu wadanda sukayi garkuwa da Umar Alhaji Manu inda suka karbi kudin fansa N170,000.

Sai kuma Tukur Ibrahim mai shekaru 35 dan karamar hukumar Borgu da Tambaya Bello mai shekaru 22 dan karamar hukumar Mashegu wadanda ake zargi da satan shanu, an ansame su da bindiga kirar AK47 guda uku da harsasai guda 8, kakin sojoji, da shanu guda 14 da tumakai 20, awaki 12 da wayar salula guda 2.

Sai kuma wadanda ake zargi da aikata fashi da makami da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, da suka hada da Kingsley Eze dan garin Zugurma a karamar hukumar Mashegu da Fatima Musa 'yar karamar hukumar Kebe ta Jihar Sokoto da Audu Dambo Baumi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso, Aminu Abdullahi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso, Muhammad Abdullahi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso. daga cikin abubuwan da aka samesu dashi sun hada da kananan bindigogi kirar gida guda 3, harsasai 11, wayoyin salula 3, da tabar wiwi da layu.

Hakazalika rundunar tayi nasarar kama wasu gaggan barayin motoci, Idowu Olaniyi da Ona Oge wanda aka sama da motar sata kirar Toyota Carina "E" mai lambar GGE 925 APP LAS. Da Daniel Ocheku Jukwai Abuja, Abdulmalik Sani AYA Abuja, Zubairu Usman Garki Durumi Abuja wadanda aka kama da mota kirar Accura MDX Jeep mai lambar MNA 435 JB.

Sai wadanda ake zargi da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba tare da yunkurin aikata laifi da makaman da suka hada da: Baye Maune dan kauyen Malani a karamar hukumar Borgu da Jesy Adamu Sabon Wuse, a karamar hukumar Tafa wadanda aka kama da karamar bindiga kirar gida guda 2 da harsasai guda 4, da katin aiki na jabu na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) da wukake da sanduna.

Da wani mutum mai suna Sanusi Aliyu mai kimanin shekara 25 dan kauyen Kutiriko Fadikpe dake karamar hukumar Bosso wanda ake zargi da yiwa wata yarinya mai suna Fatima Umar 'yar shekara 10 fyade.

Kakakin rundunar ya bayyanawa manema labarai cewar da zarar sun kammala bincike akan wadanda ake zargin, zasu gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shari'a, sannan kuma ya kara jaddada aniyar rundunar na cewar zasu cigaba da yaki da 'yan ta'adda a fadin jihar ta Neja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel