Yanzu-yanzu: Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege ya dawo majalisa

Yanzu-yanzu: Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege ya dawo majalisa

Sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, ya dawo majalisan dattawan a yanzu kuma yana zaune cikin abokan aikinsa ana zaman majalisa.

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa da safen nan sanatan ya shigo harabar majalisan inda suka dauke sandar doka. Kakakin majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi, ya tabbatar da hakan inda yace:

"A yau, wasu yan baranda karkashin jagorancin sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, sun dira cikin majalisar dattawa suka sace sandar ikon majalisa".

KU KARANTA: Yan zanga-zanga sun kai farmaki majalisan dattawa, sun dauke sandar majalisa

"Wannan abu yakar kasa ne. Kuma wani yunkuri ne na juyin mulki ga wani reshen gwamnatin tarayya Najeriya. Dukkan hukumomin tsaro su tura jami'ansu domin tabbatar da cewa an dawo da sandar"

"Majalisa na ganawar gaggawa yanzu kuma zamu kawo muku cikakken rahoton anjima" .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Neman diyyar biliyan N5bn: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Neman diyyar biliyan N5bn: Kotu ta saka ranar da zata yanke hukuncin a karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Neman diyyar biliyan N5bn: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel