Daukar dala ba gammo: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari

Daukar dala ba gammo: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari

Shugaban kasar Birtaniya, wato Firaiminista Theresa May ta bukaci a dabbaka auren jinsi daya a Najeriya da sauran kasashen rainon Ingila, kamar yadda ta shaida ma shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan.

Daily Nigerian ta ruwaito Uwargida Theresa ta bayyana haka ne a yayin taron kasashen rainon Ingila da ya gudana a ranar Talata 17 ga watan Afrilu, a Westminister, inda tace bai dace a samar da dokokin dake hana auren jinsi daya ba.

KU KARANTA: Yadda wani Dattijon biri ke biyan kananan yara N100 yana kwanciya dasu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Theresa tana cigaba da cewa sanannen abu ne cewa kasar Birtaniya ce ta fara samar da dokokin hana auren jinsi, amma tace dokokin nan ba daidai bane, kamar yadda wasu dokokin da aka kirkiresu a shekarun baya ke ci ma miliyoyin matasan zamanin nan tuwo a kwarya a yanzu.

Daukar dala ba gammo: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari
Buhari da Theresa

“Dokokin haramta auren jinsi tare da rashin kare hakkin mata da kananan Yara sun samo asali ne a kasar Birtaniya, amma a matsayita ta shugaban kasar Birtaniya na yi tir da wadannan Dokoki, ya zama wajibi mu girmama al’adun juna, amma zamu yi hakan ne tare da yi ma juna adalci.” Inji ta.

Daga karshe tace bai kamata wani ko wata ya fuskanci tsangwama ba saboda yanayin tsarin rayuwarsu na yanayin wanda suke kauna ko akasin haka ba, sa’anann ashirye kasar Birtaniya take ta taimaki duk kasar da zata sauya dokokin da suka haramta luwadi da madigo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel