Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura na sha ruwan duwatsu daga jama’a

Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura na sha ruwan duwatsu daga jama’a

A yau Talata, 17 ga watan Afrilu, 2018, gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura, ya sha ruwan duwatsu daga hannun yan sansanin gudun hijra a Agwatashi, karamar hukumar Obi, yayinda ya kai ziyara wajen.

Gwamnan ya kai ziyara sansanin yan gudun hijran ne tare da jami’an sojin jihar domin duba halin da suke ciki bayan kisan gillan mutane 32 da makiyaya suka yi ranan Lahadin da ya gabata.

Za ku tuna cewa wasu makiyaya sun kai hari kan jama’an karamar hukumar Keana, Aew da Obi inda suka hallaka da jama’a.

Lokacin da gwamnan ya fara musu Magana, wasu matasa a sansanin IDP suka fara kukunai da wakan rashin amincewa da shi. Saboda haka, sai gwamnan ya fice daga wajen.

Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura na sha ruwan duwatsu daga jama’a

Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura na sha ruwan duwatsu daga jama’a

Abin ya munana ne yayinda matasan suka fara jifan motar gwamnan da duwatsu wanda ya say an sanda suka watsa musu barkonon tsohuwa.

KU KARANTA: Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Yayinda aka tambayi gwamnan kan wannan abu, gwamna Al Makura yace hakan ya faru ne bisa ga halin kunci da kalubalen da suke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel