Wuraren tarihi 13 masu muhimmanci a garin Makkah

Wuraren tarihi 13 masu muhimmanci a garin Makkah

Kamar yadda aka saba daga lokaci zuwa lokaci Legit.ng ta kan binciko wa masu karatu wasu ababe masu fadakarwa da ilmantarwa daga fanin daban-daban. A yau mun kawo muku wasu wuraren tarihi masu muhimmanci ne a garin Makkah kamar yadda kafar Life in Saudiya ta ruwaito.

1) Daarul Arqam - A farkon zuwan addinin musulunci, Manzon Allah (SAW) ya kasance yana wa'azin a sirrance a wannan gida na Arqam. Wannan wurin mai daraja yana kusa da dutsen Safa kuma tarihi ya nuna cewa nan gidan kabilar Arqam yake.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

2) Darun Nawdah - Wannan wurin ya kasance majalisa ne wanda yan kabilar Quraysh ke taruwa domin muhawarra kan abubuwa masu muhimmanci. A wannan wurin ne aka yanke shawarar kashe manzon Allah (SAW)

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

3) Gidan Sayidina Abbas (Allah ya kara masa aminci) - Inda akayi alamar da'ira cikin hoton shine inda gidan Sayidina Abbas (Allah ya kara masa aminci) yake. Abbas (Allah ya kara masa aminci) kawun Manzon Allah (SAW) ne kuma ya bashi kariya har iya rayuwarsa.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

4) Gidan Sayyidina Abubakar (Allah ya kara masa aminci) - Wannan shine inda gidan Sayyidina Abubakar (Allah ya kara masa aminci) ya ke a garin Makkah. Daga nan ne aka fara hijira daga garin Makkah zuwa Madina.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

5) Gidan Abu Jahal - Wannan wurin shine inda gidan Abu Jahal yake a zamanin baya. Abu Jahal dan uwa ne ga Manzon Allah (SAW) amma yana daya daga cikin makiyan musulunci. Manzon Allah (SAW) ya misalta Abu Jahal da Fir'aunan zamaninsa.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

6) Gidan Sayyina Khadijah (Allah ya kara mata aminci) - Wannan da'irar da ke hanyar fita da Marwa ne inda gidan Sayyidina Khadija (Allah ya kara mata aminci) yake. A gidan ta e Manzon Allah (SAW) ya zauna har lokacin da Khadija ta rasu.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

7) Gidan Ummi Hani (Allah ya kara mata aminci) - Wurin da akayi alamar da'ira shine inda gidan Ummi Hani (Allah ya kara mata aminci) ya ke, Ummi Hani diyar Abu Talib ne kuma yar uwa ga Manzon Allah (SAW).

A wannan wurin ne mala'ika Jibrilu ya bayana ga Manzon Allah (SAW) kuma ya dauke shi zuwa Baitul-Maqdis da ke kasar Isra'ila a tafiyar da akafi sani sa Al-Isra wato tafiyar dare.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

8) Jamarat - Jamrat wasu tsaunuka ne guda uku wanda ake yin jifa a yayin aikin Hajj saboda koyi da Annabi Ibrahim (A.S). Tsaunukan guda uku sune wuraren da Shaitan ya bayyana ga Annabi Ibrahim (A.S) yayinda yake kokarin hana shi yanka dan sa Annabi Ismail (AS) kamar yadda Allah ya umurce shi amma sai ya harbe shi da dutse duk lokacin da ya bayyana. Ana kiran tsaunukan Jamarat al Wusta, Jamarat al-Aqaba da Jamarat al-Ula.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

9) Jannat-ul-Mala - Wannan shine hoton Jannat-ul-Mala wanda yana daya daga cikin makabarta mai dimbin tarihi a garin Makkah. Makabartan yana gabashin Masallacin Harami ne.

A wannan makabartan ne aka birne Sahabai da yawa da kuma wasu iyalan Manzon Allah (SAW).

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

10) Masallacin Sayyidina Aisha - Masallacin sayyidina Aisha shine wurin da uwar muminai da shiga Ihrami yayinda zata gudanar ta Umrah. Tayi Umrar ne a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya bayar da umurni hajji na karshe. Masallacin yana nan a kilomita 7.5 kudancin Makkah a hanyar zuwa Madinah.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

11) Masjid Al-Jinn - An gina wannan masallaci ne a daidai wurin da Manzon Allah (SAW) ya zana layi kuma ya umurci Abdullah bin Mas'ud (Allah ya kara masa yarda) ya dakata lokacin daya masa rakiya bayan an bashi umurnin ya karanta Suratul Jinn ga aljanu.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

12) Masjid Shajarah (Masallacin bishiya) - An gina wannan masallacin ne a daidai wurin da Manzon Allah (SAW) ya umurci bishiya ta zo kuma ta amsa kirar sa. Sai dai akwai wani masallacin mai wannan sunan a Dhul Hulayfah.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

13) Dutsen Abu Qubays - Wannan katafaren ginin da ke hoton yana kallon Dutsen Safa ne. Masana da dama sunyi itifaki cewa a saman wannan dutsen ne Manzon Allah (SAW) yayi nuni ga wata kuma ta rabe biyu.

Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah
Wuraren tarihi 13 mafi tsarki a garin Makkah

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel