Saraki bai isa ya cire son Buhari daga zukatan mu ba - Sanatoci 'yan a-mutun Buhari

Saraki bai isa ya cire son Buhari daga zukatan mu ba - Sanatoci 'yan a-mutun Buhari

Yan majalisar dattijan nan masu goyon bayan muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka hada wata 'yar kwarya-kwaryar kungiya mai suna Parliamentary Support Group (PSG) ta yi tir da korar da akayi wa daya daga cikin mambobin ta daga zauren.

Haka ma kuma 'yan majalisun dattijan da ke a kungiyar sun bayyana cewa shugaban majalisar Dakta Bukola Saraki bai isa ya cire masu son shugaba Buhari ba duk irin tuggun da zai jagoranci kulla masu.

Saraki bai isa ya cire son Buhari daga zukatan mu ba - Sanatoci 'yan a-mutun Buhari

Saraki bai isa ya cire son Buhari daga zukatan mu ba - Sanatoci 'yan a-mutun Buhari

KU KARANTA: Jihar Bayelsa na shirin maka Buhari kotu

NAIJ.com dai ta samu cewa wannan dai na zuwa ne biyo bayan dakatarwar da 'yan majalisar tayi wa daya daga cikin jiga-jigab mambobin kungiyar ta Sanatocin masu goyon bayan muradun shugaba Muhammadu Buhari mai suna Oma-Agege.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) a wata sanarwar da ta fitar ta jajantawa dukkanin daukacin mabiya shi'a almajiran Zakzaky musamman ma wadanda suka yi arangama da 'yan sandan tarayyar Najeriya yau a filin 'Unity Fountain' na garin Abuja.

Jam'iyyar wadda ta bayyana matukar jajenta, ta kuma yi Allah-wadai game da yadda suka ce gwamnatin ta tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ke cigaba da tsare shugaban mabiya mazhabar shi'ar duk kuwa da umurnin kotu a kan hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel