Akwai kwantaciyyar rikici a Jihar Zamfara – Wani ‘Dan Majalisa ya nemi ayi wata-wata

Akwai kwantaciyyar rikici a Jihar Zamfara – Wani ‘Dan Majalisa ya nemi ayi wata-wata

- Hon. Aliyu Gebi yace akwai kwantaciyyar rikici kwarai a Yankin Zamfara

- Tsohon ‘Dan Majalisar ya nemi Hukuma ta dauki babban mataki da wuri

- Gebi ya kuma gargadi sauran Jihohin da ke makwabtaka da su tashi tsaye

Mun samu labari cewa wani Tsohon ‘Dan Majalisa yace akwai rikici shigen irin na ‘Yan ta’addan Boko Haram a Zamfara wanda yayi kira Majalisar Tarayya ta kawowa Shugaban kasa matakin da ya kamata a bi na kawo zaman lafiya.

Akwai kwantaciyyar rikici a Jihar Zamfara – Wani ‘Dan Majalisa ya nemi ayi wata-wata

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari

Honarabul Aliyu Gebi wani tsohon ‘Dan Majalisar Bauchi ya bayyana cewa rikicin Jihar Zamfara yayi kamari har an kai inda aka kai don haka yace yanzu sai dai a tura Jami’an tsaro su shiga Dajin da Tsageru su ke su yi ta luguden wuta.

KU KARANTA: An tsinci makudan kudi a wajen wan hadarin mota a Bauchi

Aliyu Gebi ya kuma bayyana cewa tun a lokacin Majalisa ta 7 a 2013 Sanatan Yankin Zamfara watau Kabiru Marafa ya fada masa cewa akwai rikici a kwance a Jihar Zamfara wanda tayi kama da ta Boko Haram a Arewa maso gabas.

A wancan lokacin dai ba a dauki maganar Sanatan da kima ba sai da yanzu abin ya harzuka. Tsohon ‘Dan Majalisar ya gargadi Jihohin Katsina da Sokoto da Kebbi da su zura idanu su kuma shirya maganin wannan rikici ko su koka duka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya

Jam'iyyar ADP ta sha alwashin fatattakar APC a zaben Gwamnan wata Jiha a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel