Yanzu-yanzu: Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May

Yanzu-yanzu: Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da firam ministan Birtaniya, Theresa May, yai Litinin, 16 ga watan Afrilu, 2018 a birnin Landan.

Mataimakin shugaban kasa kan sabbin kafofin yada labarai, Bashir Ahmad, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita. Shugabannin kasashen biyu sun tattauna ne kan al'umaran Diflomasiyya tsakanin Najeriya da Birtaniya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga Firam ministan kan taimako da gudunmuwar da Birtaniya ke bawa Najeriya wajen horon jami'an sojin Najeriya domin yakar Boko Haram.

Yanzu-yanzu: Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May
Yanzu-yanzu: Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May

Abubuwa guda uku da gwamnati mai ci a yanzu ta sa a gaba sune suka fi damuna inji shugaba muhammadu Buhari a yayin da suka yi taro da Theresa May.

"Munyi kamfen ne akan abubuwa muhimmai guda uku. Tsaron kasar, farfado da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa"

"Muna da zabe shekara mai zuwa, tunanin yan'siyasa duk ya koma kan zaben amma ni abinda yafi damuna shi ne tsaro da tattalin arziki" Inji shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel